Masanin tattalin arziki Malam Nasiru Garba Dantiye, yace mizanin da kowace kasa take amfani da shi a duniya wajen auna karfin tattalin arzikinta, shine abin nan da ake kira GDP a takaice, watau mizanin dukkan kayayyakin da kasa take samarwa tare da ayyuka a kowace shekara, kuma akwai takamammun alkaluma da ake amfani da su wajen auna wannan.
Dantiye yace ga Najeriya ta sauya alkalumanta ita kadai domin kawai a ce ta fi kowace kasa a Afirka karfin tattalin arziki, ya zamo rudun kai, domin idan aka duba za a ga cewa babu wani abinda ya inganta na game da rayuwar talaka a kasa, in ban da kara sukurkucewa.
Yace wannan kididdigar rudu ce kawai.
Shi ma masanin kimiyyar siyasa, Dr. Sa'idu Ahmed Dukawa, yace alkaluman auna karfin tattalin arzikin da mahukuntan Najeriya suka fitar, na da nasaba da bukatar siyasa ta nuna cewa gwamnatin ta yi wani abin kirki.
Malamin na Jami'ar Bayero ta Kano, yace musamman a irin wannan lokaci na kusantowar zabe, 'yan siyasa zasu so su bugi kirjin cewa sun tabuka wani abin azo a gani, musamman mataki irin wannan na nuna cewa a yanzu Najeriya ta fi kowace kasa karfin tattalin arziki.
Malamin ya ce babban abinda za a duba a gani shi ne cewa, ikirarin nan da gwamnatin Najeriya ta yi na bunkasar tattalin arziki, shin ya shafi rayuwar al'umma ne ko kuma dai kawai an fito da shi ne. Yace idan har babu wani abinda ya sauya a rayuwar jama'a, to alkaluman sun zamo marasa tasiri.