Sakamakon da aka gabatar ba'a hukunce ba, ya nuna cewa jam'iyar Democratic of Struggle ko kuma PDI-P a takaice, tana bukatar kafa gwamnatin kawance bayan data lashe kusan kashi ashirin daga cikin dari na kuri'un da aka kada a ranar Laraba.
Tilas jam'iyu su samu kashi ashirin da biyar na kuri'un da aka kada, ko kuma su lashe kujeru ashirin na Majalisar dokoki kafin su iya zaben wanda zai yi musa takarar shugaba a zaben da za'a yi a watan Yuli.
Duk da haka, ana sa ran dan takarar jam'iyar PDI-P, gwamnan birnin Jakarta, Joko Widodo shine zai shugaban kasa na gaba. Yace a shirye yake a kula yarjejeniyar raba mukamai.
To amma yawancin kamfanoni masu zabu jarurruka a kasar, sun baiyana tsoron cewa yarjejeniyar daunin iko zata dagula sauye sauyen da ake yiwa tattalin arzikin kasar, da suke ganin ana bukata domin bunkasa tattalin arziki mafi girma a yankin kudu maso gabashin Asiya.