Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Arewa Kawai Ne Mafita Idan PDP Na Son Karbe Mulki A Zaben Shekarar 2023 - Dokpesi


Jigo a jam'iyyar PDP Raymond Dokpesi.
Jigo a jam'iyyar PDP Raymond Dokpesi.

Wani Jigo a jam’iyyar PDP Cif Raymond Dokpesi, ya bayyana cewa jam'iyyarsa na da kyakkyawar damar sake karbe madafun iko a Najeriya ne kawai idan ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga Arewa a shekarar 2023.

Babban jigo a jam'iyyar adawa ta PDP, kuma mai kamfanin sadarwa na DAAR mamallakin gidan talabijan na AIT da gidan rediyon Raypower, Cif Raymond Dokpesi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Daily Independent, ya na mai cewa ba bu yanda jam’iyyarsa za ta iya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2023 idan har ta gabatar da dan takara daga kudancin kasar.

A cewarsa, mambobin jam’iyyar ta PDP da ke fafutukar a bi tsarin karba-karba na shiyya-shiyya don maida tikitin takarar shugaban kasa zuwa kudancin kasar na yin hakan ne kawai saboda sun ga mambobin jam’iyyar APC na neman maida tikitin takarar shugabancin Najeriya zuwa kudu bayan kammala wa’adin shugaba Buhari a shekarar 2023.

A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa, jam’iyyar PDP na ta gudanar da tarurrukan samo sabbin dabaru don yin gyare-gyaren kan tsarinta saboda ta sami mulki a shekarar 2023.

Sai dai an dade ana ta fafutukar neman a maida mulkin Najeriya zuwa kudancin kasar a cikin jam’iyyu, ciki har da PDP.

Idan ana iya tunawa, jam’iyyar adawa ta PDP wacce ta shafe shekaru 16 a mulkin Najeriya, ta sha kaye a hannun jam’iyyar APC mai mulki ne a shekarar 2015 kuma ‘yan Najeriya suka sake zaben APC a zaben shekarar 2019.

APC, PDP
APC, PDP

To sai dai Dokpesi ya ce salon yaudara ne ‘yan Najeriya ke yi wa kan su a daidai wannan kokaci, idan aka ci gaba da cewa a maida tikitin shugaban kasa a kudu.

Dokpesi mai shekaru 70 a dunya ya ce la’akari da gogewarsa a fannin shirya gamgamin yakin neman zabe a wannan kasa, zai iya cewa damar samun madafun iko ga jam’iyyarsa ta PDP ba ta wuce tsaida dan arewa a matsayin dan takara ta ba.

Har ila yau, Dokpesi ya ce ya kamata PDP ta yiwa kanta karatun ta natsu cikin gaskiya, la’akari da yadda tsohon shugaban kasa cif Olusegun Obasanjo daga kudu maso yamma ya yi shekaru takwas kan karagar mulki, Goodluck Jonathan daga kudu maso kudu shi ma yayi shekaru shida wanda ta kai jimlar shekaru 14 a madafun iko.

"Idan ana iya tunawa, a wani gefe kuma, marigayi tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar’Adua daga arewa ya yi shekaru kusan uku kan kujerar mulki kafin rasuwarsa, don haka akwai tazarar shekaru 11 har yanzu tsakanin mulkin kudu da Arewa" in ji Dokepsi.

Kamar yadda Dokpesi ya bayyana, idan da a zaben shekarar 2019, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya sami nasara a zaben ne, da zai dawo a shekarar 2023 don zai so yin wa’adi na biyu.

Don haka ne Dokpesi ya bukaci mutane su yi hakuri har zuwa lokacin da mulkin Najeriya zai koma kudu, yana kuma mai shawartar PDP da ta fito da dan takarar shugaban kasa daga Arewa a shekarar 2023.

Dangane da fafutukar neman shugabancin kasar na 'yan kabilar Igbo, Dokpesi ya ce yana ganin ya dace a ce yankin kudu maso gabas ya samar da shugaban kasa saboda itace shiyya daya tilo ta kudu da ba ta yi hakan ba tun bayan dawowar tsarin mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, to amma yankin ba zai iya samun nasara ba idan aka ba shi tikitin takarar shugaban kasa a daidai wannan lokacin.

XS
SM
MD
LG