Janar Babangida ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da gidan talabijan na Arise na safiyar a radar Juma’a, inda ya ce yana da yakinin cewa, Najeriya za ta gyaru sai dai matsalar ita ce ‘yan kasar ba sa ganin hakan.
A cewar janar Babangida, matsalar da ta fi kassara Najeriya ita ce rashin shugabanni da suka iya shugabanci nagari da kishin kasa yana mai cewa, idan aka samu shuwagabannin masu tafiyar da al’umma a duk manufofin su, za’a samu cigaban da ake nema.
A game da batun wanda zai shugabanci Najeriya daga shekarar 2023, Janar Babangida ya ce, akwai mutane kusan 3 da yeke hangen za su iya jan ragamar shugabancin kasar wadanda ke da shekaru daga 60.
Amma bay bayyana sunken mutant ba.
Daga cikin abin da Janar Babangida ya ce ya kamata mutumin da zai shugaban Najeriya ya kamata ya kware akai shi ne mutumin ya zamanto yana da kwarewa a fannin tattalin arziki.
Haka kuma, IBB ikirarin ceza gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba ta hukunta barayin da ke ruf da ciki da kudin al’umma yana mai cewa, yanayin da ake ciki a kasar tamkar ana maida barayi ’yan gata ne inda ya kara da matsalar cin lanci da rashawa ta rubanya a zamanin mulkin Buhari.
Mukarabban gwamnatin da shugaba Buhari ke jagoranta aka fi zargi da karbar rashawa idan aka kwatanta da gwamnatin Babangida ta mulkin soji musamman ta wajein yaki da rashawa fiye da na Buhari, yana mai cewa, barayin gwamnati sun samu sakewa a wannan karon.
Kazalika, janar Babangida ya ce a zamantin mulkinsa na soji, sai da aka hukunta wani gwamnan mulkin soji da ya wawure kudadden da aka kiyasta ya kai naira dubu 313, yana mai cewa a wannan gwamanti da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta, an ki hukunta barayin biliyoyin naira suna yawo.
Har yanzu fadar gwamatin Najeriya ba ta ce uffan kan ikirarin tsohon shugaban kasar ba.
Daga karshe dai, Janar IBB ya yi kira da gwamnatin kasar ta sassauta tsare-tsarenta ta fuskar tattalin arziki don shawo kan matsin da ake ciki a halin yanzu wanda ya jefa 'yan kasa cikin halin kakani-kayi.
Idan ana iya tunawa, janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda dan asalin jihar Neja da ke arewacin kasar ne, ya shugabanci Najeriya tsakanin shekarar 1985 zuwa shekarar 1993.