Trump ya kara da cewa 'yan jarida ne suka sauya ma'anar kalaman na sa.
Ya kuma rubuta a shafinsa na Twitter cewa rahotannin CNN sun ba da labarin akan jawabinsa cewa ya ce shugaba Obama da 'yar takarar Democrat su ne suka kafa ISIS da MVP. Wanda ke nuna tabbatacin cewa ba su fahimci ba’ar da ya yi ba.
Wannan suka da Trump ke sha nan da can, ta jefa shi cikin tsaka mai wuya ba ma a wurin 'yan jarida kadai ba har a tsakanin 'yan jam'iyarsu.
Wannan shi ne karo na biyu a cikin wannan mako da wasu kusoshin jami’iyarsa ta Republican suka fito suna bayyana matsayarsu inda suka ce ba za su kadawa Trump Kuri’arsu ba.
Kimanin 'yan jami’iyar 70 ne cikinsu har da tsaffin wakilan majalisa da manyan jami’an gwamnatotcin shugaba Reagan da shugaba Bush suka aike da takardunsu ga shugaban kwamitin zartarwa na Republican, Reince Priebus, cewa jami’iyarsu ta mai da hankali wurin taimakawa masu mata takarar majalisar wakilanta da na majalisar dattijai a maimakon Trump.