Hedkwatar tsaron Najeriya tayi karin haske kan wasu gungun motocin yaki na Majalisar Dinkin Duniya da aka gani a wasu jihohin kudancin
kasar, da hakan ya janyo cece- kuce a kafofin sada zumunta.
Kakakin rundunar tsaron Najeriyar, Brigediya Janar Tukur Gusau cikin
wata sanarwa da ya sanyawa hanu, yace Najeriya na bada gudunmuwar
dakaru ga Majalisar Dinkin Duniya a ayyukan samar da zaman lafiya
daban daban
Na baya bayannan shine ga rundunar Majalisar dake Abyei a kudancin
Sudan, wacce wani hafsan Najeriya Manjo Janaral Olufemi Benjamin
Sawyer kewa jagoranci.
Janar Gusau yace yana da kyau a fahimci cewa Majalisar Dinkin Duniya
bata da wasu dakaru na dindindin, amma dai kasashe ne ke yin karo -karon
dakaru yayin da duk bukatar hakan ta taso.
Saboda haka manyan motocin yakin da aka gani da ma sauran kayayyakin
fada na sojoji a kudancin kasar dake da fenti da kuma tambarin
Majalisar Dinkin Duniyar za a kaisu Sudan ta Kudu ne ta cikin tashar
jiragen ruwa dake Warri
Hedkwatar tsaron karkashin jagorancin janar Irabor na baiwa 'yan Najeriya tabbacin cewa, Najeriya bata fuskantar kowane irin barazanar tsaro da har ka iya kaiwa ga kawo sojojin kasar waje.
Bayanan Rundunar Tsaron Najeriya Akan Motocin Sojin MDD A Kasar
Shelkwatar Rundunar Tsaron Najeriya ta bayyana cewa, bata fuskantar wata barazanar tsaro da zata kai ga kawo sojojin kasashen waje cikin kasar.
Abuja, Nigeria —