Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Saman Najeriya Ta Karbi Sabbin Jiragen Yaki Biyar


Super Mushshak
Super Mushshak

Rundunar sojojin saman Najeriya ta karbi sabbin jiragen yaki biyar cikin goma da gwamnatin tarayya ta sayo daga kasar Pakistan.

Sabbbin jiragen yakin biyar sun isa sansanin sojojojin saman Najeriya dake Kaduna.

A baya dai sojojin saman Najeriya sun sha fama da matsalolin jiragen yaki, musamman lokacin da ‘yan kungiyar Boko Haram ke ta rawar gaban hantsi a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

Babban hafsan hafsoshin mayakan saman Najeriya, Air Marshall Sadiq Abubakar, ya ce shekaru masu yawa da suka gabata basu taba ganin samun nasara a fannin jiragen yaki irin yanzu ba.

Kwararre kan jiragen yaki, Baba Gamawa mai ritaya, ya ce wannan lamari zai taimakawa sojan saman game da yakin da suke da ‘yan ta’adda.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG