Wa’adin gudanar da harkokin gwamnatin Amurka ya cika ba tare da an cimma jituwa kan samar da kudin tafiyar da gwamnati ba.
Da yammacin jiya Juma’a cibiyoyin gwamnatin Amurka suka fara shirye-shiryen dakatar da harkokin gwanatin da basu da muhimmanci sosai kafin wa’adin kudaden gudanar da ayyukan gwamnati ya kare karfe goma sha biyun dare agogon Washington.
Yunkurin Majalisar Dattawa na kada kuri’ar hana dakatar da harkokin gwamnatin ya ci tura. A halin yanzu dai ba a san irin tattaunawar da ake yi a bayan fage don shawo kan lamarin ba.
Tun da farko, wata ganawa da aka yi tsakanin shugaba Donald Trump da jiga-jigan ‘yan jam’iyyar Democrat a Majalisar Dattawa ta ka sa kaiwa ga daidaitawa.
Yan Jam’iiyar Democrat dake majalisar Dattawa sun ki bada hadin kai saboda su matsa lamba a warware matsalar bakin haure da kuma tsarin kashe kudi.
Yan Republican na zargin takwarorinsu na Democrat da kin mayar da hankalinsu kan abinda yafi muhimmanci.
Facebook Forum