Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hankalin Buhari Ya Koma Kan Neman Maslaha Tsakanin Makiyaya da Manoma


Wani Bafullatani da dabbobinsa a Nijar
Wani Bafullatani da dabbobinsa a Nijar

Sakamakon rashin jituwa tsakanin makiyaya da manoma a jihohin Adamawa, Taraba, Binuwai da ma wasu, ya sa hankalin shugaban kasa ya koma akan lalubo bakin zaren matsalar da zummar samun zaman lafiya mai dorewa a duk fadin kasar

Hankalin fadar shugaban Najeriya ya koma kan neman bakin zaren warware asarar rayuka sakamakon rashin jituwa tsakanin Fulani makiyaya da manoma musamman a jihohin Binuwai, Taraba da Adamawa.

Gwamnatin Najeriya da ta tura baban sifeton 'yan sanda Ibrahim Idris zuwa Bnuwai don kwantar da tashin hankalin da ya kunno kai, ta kuma dauki matakin kawo masalaha ta hanyar kafa gandun dajin kiwon shanu a jihohin da lamarin ya shafa.

Gwamnan Binuwai Samuel Ortom da ya jagoranci shugabannin siyasa da na gargajiya na jiharsa har suka gana da Shugaba Buhari ya ce bai goyi bayan kafa gandun daji ba amma makiyaya na iya sayen fili su yi gonakin kiwo. Ya ce jiharsa ba ta da kadada dubu goma da za ta bayar. Injishi, wasu jihohi masu fili ka iya basu.

Hatta kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ba ta ganin kafa gandun shi ne zai zama masalaha mafi inganci fiye da dawo da burtalin shanu na gargajiya ba.

Shugaban kungiyar, Muhammad Kirwa Ardon Zuru ya ce a Najeriya akwai burtalin shanu idan za'a bi burtalin a farfado dashi babu wani Bafillatani da zai dauki shanunsa daga Sokoto ya nufi Enugu.

Matsala ce ta tilastawa mutum fita da dukiyarsa, injishi. A gyara abun da ya rage na burtalin shanun da manoma basu cinye ba, Fulani zasu dawo su zauna saboda sun gaji da wahalar da suke fama da ita. Ya ce fadan makiyaya da manoma ya na daukan salo daban daban. A wani wurin ya zama tamkar fadan addini tsakanin Kiristoci da Musulmai, a wani wurin kuma ya zama na kabilanci.

Ga karin bayani daga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG