Ya samu nasarar yin hakan ne a lokacin da kungiyarsa ta Juventus ta doke Dynamo Kiev a gasar cin kofin zakarun turai.
Ya dai zira kwallon ne cikin ruwan sanyi, wacce aka doko ta daga kuryar gefen ragar.
An tashi a wasan da ci 3-0.
‘Yan wasa uku ne dama suke gaban Ronaldo a jerin wadanda suka yi fice wajen yawan kwallaye a riga, akwai kuma yiwuwar ya wuce su kafin karshen wannan kakar wasa idan har tauraruwarsa ta ci gaba da haskakawa.
Yanzu haka Pele wanda ke da kwallaye 767 na gaban Ronaldo da kwallaye 17 yayin da Romario ke da kwallaye 772, wato yana gaban Ronaldo da kwallaye 22 kenan.
Josef Bican ne ke gaba da yawan kwallaye da ba a tabbatar ba, amma rahotanni sun yi kiyasin yana da kwallaye akalla 805.