Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Lashe Gasar La Liga Ta Bana


Real Madrid
Real Madrid

Real Madrid ta lashe gasar La Liga ta kasar Spain karo na 34

Kungiyar kwallon kafar Real Madrid ta lashe gasar La Liga ta kasar Spain ta bana, bayan da a yau Alhamis ta doke Villarreal da ci 2-1, wanda ya ba ta tabbacin tazarar maki 7 a saman teburin gasar tsakanin ta da Barcelona da ke bin ta, wadda ita ko ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Osasuna mai ‘yan wasa 10.

Real Madrid
Real Madrid

Kafin dakatar da wasanni saboda annobar coronavirus dai Barcelona ce ke jagorancin teburin gasar da tazarar maki 2 tsakaninta Real Madrid da ke binta, to sai dai lamarain ya sauya ne bayan da Madrid din ta yi nasara a dukkanin wasanninta 10 na gasar da ta buga tun sa’adda aka dawo fafata wasanni baya hutun na coronavirus.

Wannan ne karo na 34 da kungiyar ta Madrid ta ke lashe gasar ta La Liga, duk da yake dai shi ne na farko da ta lashe a cikin shekaru 3, kuma na farko tun sa’adda shahararren dan wasanta Cristiano Ronaldo ya bar ta, haka kuma shi ne na farko tun bayan dawowar kocin kungiyar Zinedine Zidane karo na 2 bayan barin kungiyar da yayi da farko.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane

Kungiyar ta yi bikin murnar daga kofin ne salun-alun sakamakon rashin ‘yan kallo da masoyan kungiyar kamar yadda aka saba a filin wasa, sakamakon dokokin coronavirus.

Real Madrid
Real Madrid


To sai dai hakan bai hana ‘yan wasan kungiyar da wasu jami’anta da ke filin yin murna ba iya yadda hali ya bayar, ciki ko har da daga kocinsu Zidane da cilla shi sama har sau uku.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG