Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudi Bai Kare Shi Daga COVID-19 Ba: Cristiano Ronaldo Ya Kamu Da Cutar Corona

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:41 0:00

Cristiano Ronaldo, daya daga cikin manyan tauraruwar kwallon kafa kuma daga cikin shahararrun ‘yan wasa a duniya, gwaji ya tabbatar cewa ya kamu da cutar coronavirus, kungiyar kwallon kafa ta Portugal ta sanar a ranar 13 ga Oktoba.

Bayan da Ronaldo, dan wasan gaba a Juventus, ya kamu da cutar corona, sai duk sauran ‘yan kulob din su ka yi wani sabon gwaji, amma babu wanda aka samu da cutar.

Ronaldo ya samu dala miliyan 109 a 2019. A cewar mujallar Forbes, hakan ya sa ya zama dan wasan kwallon kafa na biyu da ya fi daukar albashi a duniya, bayan Lionel Messi.

Bayan kakannin wasa tara tare a Real Madrid, Ronaldo ya rattaba hannu kan wata yarjajjeniya ta shekaru hudu a 2018 da Juventus ta kasar Italiya. Wannan ya sa yana samun dala miliyan 64 a shekara.

XS
SM
MD
LG