Ana ci gaba da yada rade-radi da hasashen kungiyar da za ta iya kasancewa sabon mazauni ga shahararren dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona Lione Messi, a yayin da manazarta ke ganin Manchester City ta Ingila ce ta fi dama akan sauran kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan.
Kungiyar PSG ta kasar Faransa ta dade tana tattaunawa da mahaifin Messi, wanda shi ne jami’in kasuwancinsa, haka kuma ta sabunta tattaunawar a ‘yan kwanan nan, akan yiwuwar komawarsa kungiyar, kuma har ta aike masa da bukatar a rubuce a ranar Talata da ta gabata.
A daya bangare kuma, kungiyar Juventus ta kasar Italiya ma ta soma shiryawa tare da tanadin makudan kudade shiga fagen dagar samun Messi, ta yadda za ta kafa tarihin hada shi kungiya daya da Ronaldo.
A wannan karshen makon ma ana ta baza rade-radi da rahotannin da ke tabbatar da cewa Messi na matukar bukatar barin kungiyarsa ta Barcelona, a yayin da ita kungiyar ta ke bukatar ci gaba da zamansa tare da ita.
Barcelonar dai ta kafe akan cewa Messi ba na sayarwa ba ne a yayin da kwantaraginsa zai kai har ya zuwa karshen kakar wasanni mai zuwa. To sai dai ta yiwu ta iya sayar da shi idan ta sami makudan kudade da suka kai yuro miliyan 700 da ke kunshe a yarjejeniyar sayensa da ke cikin kwantaragin na sa.
Lionel Messi dan kasar Argentina mai shekary 33, ya lashe lambar gwarzon dan kwallon duniya na shekara har sau 6 a zamansa kungiyar ta Barcelona.
Facebook Forum