'Yan wasan tsakiya na kasar Sifaniya Rodri da Aitana Bonmatí sun lashe kyautar Ballon d'Or ta maza da mata a ranar Litinin a matsayin gwarazan ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, yayin da Real Madrid ta kauracewa bikin wanda ya cika makil da fitattun taurarin ‘yan wasa a birnin Paris.
Rodri mai shekara 28 ya lashe wannan kyautar mai daraja a karon farko bayan ya taimaka wa Manchester City lashe Gasar Premier da kuma zama fitaccen dan wasa a nasarar kasar Sifaniya a Gasar Zakarun Turai.
Ya gaji Lionel Messi na Argentina wanda ya lashe kyautar sau takwas ciki har da bara, kuma ya doke Vinícius Júnior na Real Madrid wanda ya zo na biyu, sakamakon da ya sa kungiyar ta nuna fushinta ta hanyar kauracewa bikin.
Madrid da 'yan wasanta baki daya ba su halarci bikin ba, sannan sun shiga shafukan sada zumunta don nuna bacin ransu.
Bonmatí mai shekara 26 ta ci gaba da rike kyautarta bayan ta taimaka wa Barcelona lashe gasar La Liga ta Sifaniya da kuma Gasar Zakarun Turai a bangaren mata.
Dandalin Mu Tattauna