Wannan shine karo na farko tun bayan rikicin shekaru biyu kenan d a wadanda suka yi hasarar rayuka da duniya suke ganin gudumawa ta farko. Adamawa tana cikin jihohi kamar hudu a arewacin Najeriya da rikicin ya shafa. Sauran jihohin sune Buachi, Kaduna da kuma Sokoto.
Borin ya biyo bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa, wanda ya nuna cewa shugaba Goodluck Jonathan ya sami gagarumar nasara. Abinda ya janyo zargin cewa an tafka magudi dalilinda masu zanga zangar suke ganin shugaban kasa ya sami nasara.
Da yake magana da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz, a Yola, shugaban kwamitin raba kudaden Alhaji Mohammadu Ajuju Jimeta, yace wannan ba diyya ba ce, domin idan mutum yayi bari, ba zai iya ya kwashe duka ba, saboda haka wannan ba diyya bace, tallafi ne ga wadanda suka yi hasara lokacin da aka yi rikicin.
Wadanda suka amfana karkashin shirin a karamar hukumar Yola ta arewa kamar su Halliru Umar, da Samuel Onora sun bayyan farin cikinsu da samun wannan tallafi.