Mutane da yawa sun mike suka fice daga wurin wannan taron, wasu kuma suka fara ihun nuna rashin yarda a bayan da shugaban Kungiyar Matasan Arewa, Jibril Lawal Tafida, ya fara tabo batun cewa su na zama tare da shugaba Jonathan kuma zai mika koke-koken matasan na arewa gare shi.
Da yawa daga cikin matasan da suka tattauna da wakilinmu sun ce ba abinda aka ce musu za a yi a wurin taron ba ke nan. Ahmed Hassan Rufa'i yace an kira su ne bisa hujjar cewa wai za a tattauna samun hadin kan matasan arewa ne, amma sai daga baya suka gane cewa wai a kan a goyi bayan shugaba Jonathan ne.
Haka kuma yace an yi a kan za a tattauna matsalolin arewa, amma kwatsam sai suka ji mai kiran taron a jawabinsa ya koma batun cewa yana tare da shugaba Jonathan kuma zai kai kukarsu gabansa.
Sai dai malam malam Jibril Tafida ya musanta cewa ya kira taron ne don neman goyon baya ma shugaba Goodluck Jonathan.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Lawal Isa Ikara, ya aiko mana daga Kaduna.