A dai dai lokacinda gwamnatin take kai musu wannan doki, sai ga shi an sami labarin cutar amai da gudawa ta bulla a wasu sansanonin da 'yan gudun neman mafakan suke a Namu, Kwande, da bakin cibiya, cikin karamar hukumar Qwanpam.
Da take magana da wakiliyar Sashen Hausa Jamila Lawal, tace suka cikin damuwa kwarai, da suka hada d a rashin kudi, ka mata masu juna biyu kusan sittin wadanda suka haifu a sansanonin ga kuma karancin kiwon lafiya cikin yanayi d a suke ciki. Tace ko sisi mutum ba ya iya tayarwa balle suyi tunanin baiwa yara ko da kudin kashewa. Da take amsa tambayar batun makaranta sai tace ai basu da kwanciyar rai balle kuma a yi zancen unifom da yara domin zuwa makaranta.
Da yake magana kan gudumawarda gwamnatin jihar Flato ta samar, sakataren hukumar agajin gaggawa na jihar Flato Alhassan Barde, yace tallafawa 'yan gudun hijirar ya zama wajibi domin baya ga kasancewarsu mutane daga jiha makwabciyar jihar wadanda suka fada cikin mawuyacin hali, ita jihar Flaton ba a juma ba da ta sami kanta cikin irin wannan yanayi.
Mr. Barde yayi alkawarin gwamnatin zata tabbatar da cewa kayayyakin agajin sun kai ga wadanda aka saya dominsu.