Mahaifiyar ta mai suna Idella Carey ta ce sunan matar Miriam Carey kuma shekarun ta 34. Mahaifiyar ta shaidawa gidan talbijin din ABC cewa 'yar ta, ta yi fama da matsalar rashin lafiya mai nasaba da kunci da damuwa bayan haihuwar 'yar ta a cikin watan agustan da ya gabata, wadda da turanci a ke kira Postpartum Depression.
Majiyoyin 'yan sanda sunce matar ta na da tarihin tabun hankali kuma a cikin kan ta, ta na jin kamar shugaba Barack Obama ya na yi ma ta magana.
'Yan majalisar dokoki da ma'aikatan majalisar sun yi awa daya a killace a wani daki a lokacin da abun ke faruwa a ranar alhamis, amma 'yan sanda sun ce babu wata barazanar da aka yiwa 'yan majalisar dokokin daga cikin ginin majalisar.
Hukumomi sun ce jami'an 'yan sanda biyu sun ji ciwo kuma ana kyautata cewa za su samu sauki. Kuma ba sa jin cewa al'amarin ya na da nasaba da matsalar rufe wasu ma'aikatun gwamnatin da ake fama da ita yanzu haka a kasar Amurka.