A cewar wani mazaunin karamar hukumar wanda ya nemi a sakaye sunanshi, lamarin ya fara ne ranar Talata a lokacin da aka kashe wani mutum misalin karfe shida na yamma a lokacin da yake tare da abokinshi.
Jami’an tsaro sun bayyana har suka samu nasarar kwantar da hankulan jama’a, sai dai da aka bi jinin dake kasa, zuwa yayi rugar wani Fulani wanda yaki barin jama’a su shiga dakinsa. Da jama’a suka yunkura, sai ya bude musu wuta da bindiga samfurin AK-47, nan da nan sai fada ya tashi harda kone-kone.
Duk da cewa jami’an tsaro sun bayyana, tarzomar bata kwanta ba har aka kashe mutane 8 kuma aka kona gidajen jama’a da yawa.
A halin yanzu mata da yara sun kauracewa garin.
Wani Fulani wanda ya bukaci a sakaye sunanshi ya fadi abunda ya faru daga nashi bangare.
“Shekaran jiya Fulani makiyaya dake kiwo a kasar Mangu, aka kora musu shanu, aka kashe wani Bafillatani daya. Yau da safe, wasu daga cikinsu sun koma neman shanun, shine rikici ya sake barkewa aka bisu ana harbinsu wasu daga cikinsu mutum 5 an kashe su.”
“Su sojojin suna nan, a gabansu aka kona rugagen Fulanin, a gabansu aka kashe Fulanin, kuma a gabansu yanzu ake rusa gidajensu inda suke zaune”, a cewar bafillatani.
Sashen Hausa na Muryar Amurka yayi kokarin jin ta bakin Jami’an tsaro amma babu nasara.
Sannan al-ummar yankin mahadar Yelwan Shandam da Langtang ta Kudu sun bukaci a girke musu jami’an tsaro, saboda kwanton bauna da kashe mutane da akeyi a hanyar.