Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Tsaro ta Jihar Filato ta Kama Wasu da Zargin Basu da Izinin Zama a Kasar Najeriya


Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya.

Rundunar tsaro a jihar Filato ta cafke wasu 'yan asalin kasar Jamhuriyar Niger akan zargin basu da takardun zama cikin kasar.

Kakakin rundunar tsaron a jihar Filato Keften Ikedichi Iweha yace tun can dama suna sa ido akan mutanen da ta cafke kuma tuni ta mikasu ga hukumar shige da fice domin su cigaba da daukan matakan da suka kamakata.

Yace sun samu mutane tamanin da biyu da suke zarginsu da wasu abubuwa. Cikin mutanen 34 daga kasar Niger suke. Sauran kuma suna nan a hargitse domin akwai masu uwa ko uba daga Najeriya. Su 34 basu da takardun zama cikin kasar.

Tun farko hukumar tana sa ido a wasu wurare musamman cikin babban birnin jihar wato Jos domin dakile duk wani shirin ta'adanci.

Kwamishanan sufuri na jihar Filato Alhaji Abubakar Dashe yace babbar matsalar da suke samu ita ce yadda ake samun motoci suna sufuri tsakanin kasar Niger da Jos ba tare da sanin hukumomin shige da fici ba, kwastan da masu kiwon lafiyar iyakar kasar. A cikin garin Jos akwai tashoshi biyu na zuwa Niger.

Yace mutane na shiga kasar ba tare da an tantancesu ba. Ga maganar cutar ebola ga na rashin cikakken tsaro dalili ke nan da suka sa ya samu hukumomi su yi wani abu. Yace wadansu 'yan Niger suna daukan makamai suna bin mutane gida gida suna kashesu.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG