Kakakin rundunar 'yansandan jihar Nasarawa ASP Umar Ismaila Numan ya shaidawa wakiliyar Muryar Amurka cewa rikicin tsakanin makiyaya ne da manoma.
Numan yace rikici ne wanda suna fama dashi tsakanin Fulani da kabilar Eggon. Eggon manoma ne Fulani kuma makiyaya ne. Wajen mako guda da ya wuce aka fara samun rikici cikin wasu kauyukan gabashin Lafiya sai yanzu kuma ya fara shigowa gari. A wani kauye Arikiya sun samu labarin a bugi Fulani. 'Yansanda sun isa wurin amma biyu sun mutu sauran kuma suna asibiti. Akwai wani kauyen ma da aka bugi Fulani su ma suna asibiti. Akwai rahoron dake cewa Eggon suna bin gidajen Fulani suna konawa.
Tun lokacin da aka fara samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Nasarawa rundunar 'yansandan ta kafa kwamitin tsaro suna kuma tura jami'ansu wurare daban daban domin kwantar da rikicin da ka kunno kai. Yanzu zasu kara dakaru domin shawo kan lamarin.
Sakataren kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Nasrawa Alhaji Muhammed Useini yace yanzu haka wasu Fulani suna gudun hijira a wasu kananan hukumomin jihar. Kwana uku da suka wuce 'yan kungiyar Mbase ta kabilar Eggon suka farma Fulani a duk yankin kasar Eggon. Sabili da haka Fulani sun gudu sun shiga wasu yankunan jihar har da ma Shendam a jihar Filato. Alhaji Useini na cewa an kashe mutum shida duk Fulani kana akwai wasu kuma da suka bata ba'a gansu ba.
Amma shugaban cigaban kabilar Eggon na kasa Mr. Chris Manman yace babu wata matsala tsakanin kabilarsa da Fulani. Yace abun da ya sani shi ne kwanaki uku da suka wuce Fulani sun fara kwashe kayansu suna barin kasar Eggon. Basu san menene yake zuwa ba da yasa suna kaura. Yace batun kashe-kashe kullum ana kashe mutane yayin da ake fashi da makami. Ya sani a wani kauye wasu barayi sun kashe Fulani sun kuma tafi da babur dinsu. Yace barayi ne suka yi kashin. Kwanakin baya da matasa suka farma Fulani mutane Eggon ne suka kaisu asibiti. Idan an samu damuwa kamata yayi a zauna a tattauna. Kwashe kayansu da suka yi ya nuna suna da wata manufa.
Ga rahoton Zainab Babaji.