Jirgin da ya fito daga Saudiya dauke da fiye da alhazai dari biyar bai iya sauka ba domin rashin wutar lantarki. Dole ya karkata kai zuwa filin saukar jirage na Malam Aminu Kano dake Kano. A can Kano aka saukar da alhazan. Inji wasu alhazan haka aka bar su ba abinci ko wurin sa kai har kusan karfe hudu na asuba kafin a basu wani abun tabawa.
Sanadiyar rashin tanada masu wurin sa kai a filin jirgin mutane fiye da dari biyar suka kwana a wajen Allah inda suka ta yin fama da sauro. Wani daya daga cikin ma'aikatan jirgin ya yi alkawarin zuwa samo masu abinci da motoci da zasu kaisu otel inda zasu kwana, amma sai ya bace.
To sai dai hukumar alhazai ta jihar Adamawa ta ce ba laifin masu jirgin ba ne domin sun cika aikinsu. Matsalar rashin wuta ta jawo kaisu Kano. Sakataren hukumar Alhaji Salihu Danjuma ya ce wannan abu ne da jihar ya kamata ta duba domin a guji na gaba.
An ce wannan ba shi ne karon farko ba da filin jrigin na Yola ya samu matsalar wutar lantarki. Jami'an filin sun ce lamarin ya fi karfinsu.
Ga Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.