A cikin wani rahoton da ta bayar, kungiyar Amnesty ta ce kamfanin Shell yana yawan dora laifin gurbacewar yanayi a sanadin tsiyayar mai a kan 'yan yankin na Niger Delta dake fasa bututu domin satar mai.
Amnesty ta ce kokarin kaucewa fuskantar shari'a ne ya sa kamfanin na Shell yake yawan dora laifin tsiyayar mai a kan matasan yankin Niger Delta.
Wakilin Sashen Hausa, Lamido Abubakar, ya zagaya a cikin yankin domin jin ra'ayoyin jama'a game da wannan rahoto na kungiyar Amnesty, ya kuma aiko mana da wannan rahoto...