Yayinda aka aika da kungiyoyin zuwa jihohin da suka kamu domin su kare barkewar, ministan yace yanayin da ya kawo barkewar kwalera basu karkashin ayyukan ma’aikatar lafiya ta tarayya, amma na wadannan jihohin da wadansu ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Yayinda yake Magana ta bakin jami’in watsa labarai na ma’aikatar Mr Dan Nwomeh, Farfesa Chukwu ya kara da cewa, ko da yake aikin kare kamuwa da cutar basu karkashin ma’aikatar gwamnatin tarayya duk da haka ma’aikatar zata yi iyakar iyawa wajen jinya da ganin cewa ba a sake samun irin wannan matslar bat a wajen yin aiki da jihohin da kuma wadansu ma’aikatun gwamnatin tarayya domin kauda matsalar.
Shi ma da yake bayani a kan matsalar cutar kwalara a garin Ibadan, Dr Oladimeji Olayinka, kodinato na kudu maso yamma, na shugaban kananan asibitoci na kasa, ya bayyana cewa babu wata allurar rigakafi da akayi domin kare cutar kwalera. Yace abu mafi muhimmanci da ake bukata domin kare kamuwa da cuta da kuma yaduwarta shine ruwa mai tsabta. Yace ma’aikatar ta aika da maganin sha na ruwa ga jihohin dake kuduncin kasar, kamar yadda jihohin dake wannan sashen suka sayi wannan magani da yawa a matsayin matakin kare wannan matsala.
Dr Olayinka yace yin amfani da maganin ruwa bisa ka’ida ga marasa lafiya masu fama da kwalera, zai taimaka wajen maida ruwan jikinsu kuma ya taimaki jiki yakin cutar kamin mara lafiyar ya sami magani a asibiti.
Kodinatan sashin, wanda yace ma’aikatar tana binciken dukan ruhotannin cutar kwalera a yankin, yace, raguwar ruwan jiki ne ke kashe mutane, musamman ga yara. Saboda haka yace ana bukatar kula wajen ganin an ba wanda ya kamu da cutar kwalara ruwa domin shine zai ceci ran mutumin.