Da ya ke bayani ma wakilinmu a Abuja Sale Shehu Ashaka, Kauran na Bauchi ya ce za a dau wannan matakin ne saboda akasin da aka samu da ya hada har da salwantar rayuka da dukiyoyi sanadiyyar irin wadannan gine ginen. Ya ce wasu gidajen an fara gina su tun sama da shekaru goma zuwa goma sha biyar; wasu ma har shekaru 20 ko fi a birnin na tarayya amma ba a gama su ba, in ji Ministan.
Irin wadannan gine ginen, in ji shi, sun zama wuraren da miyagu ke kulle kullensu na cutar da al’umma. Hasali ma, in ji Ministan, dokar Birnin Tarayya ta tanaji tabbatar da tsafta da kuma ingancin muhalli, ta yadda idan an fara gini to a kammala shi cikin shekaru biyu. Ya ce idan an bar gini ya yi shekara da shekaru ya na shan ruwa da zafin rana to kwarinsa zai ragu ta yadda idan an kammala shi ma wata rana ya na iya faduwa kan mutane.
To saidai Ministan ya yi bayanin cewa ba haka kawai za a rushe gini ba; sai an tabbatar da hadarin da ke tattare da barinsa. Kuma za a yi hakan ne ta wajen gwajin da ake kira a Turance “Integrity Test” wato gwada kwarin gini da kwararru ke yi. Idan ta tabbata cewa gini ba kwari sai a rusa a sa mai ginin ya sake wani. Kauran Bauchi ya ce za a yi wannan aikin ne babu sani ba sabo kuma ba son kai saboda amfanar al’umma da kasa baki daya.