Pascal Patrick, wanda shi ne mai ba shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya shawara a kan wasannin matasa, yace tun da farko, sai da suka tsaya suka tabbatar da cewa 'yan wasan da za a zaba, sune suka dace, kuma shekarunsu yayi daidai da wadanda ake bukata.
Yace mai koyar da wasanninsu, Manu Garba, da mataimakansa kamar su Amunike, sun koya musu wasanni irin na zamani da aka sani a duniya baki daya, watau salon buga kwallo na taba-in-taba, ba irin kwallon nan da aka sani na kowa yayi ta gaban kansa ba.
Pascal Patrick yace wadannan 'yan wasan, an maida hankali sosai kafin a dauko su daga 'yan wasan kasa da shekara 13 na Najeriya a baya, kuma 'yan wasa ne da suka fito daga kowace kusurwa ta Najeriya.
Ya bada shawarar cewa idan ana son dorewar irin wannan nasara, to shi mai koyar da 'yan Golden Eaglets, Manu Garba, a kara masa matsayi zuwa ga mai koyar da 'yan wasan kasa da shekara 20, watau Flying Eagles, domin ya tafi gaba da wadannan yara. Su kuma mataimakansa su sake zabo yara su koyar da su dabaru irin wannan na bana.
Shahararren dan kwallon yace idan an yi haka, to nan da shekaru kadan, za a samu 'yan wasa bangaren manya wadanda zasu burge kowa a duniya.
Ga cikakken bayanin da Pascal Patrick.