Zahid Muhammad mawaki hip hop, yace ya kara sana’ar daukar hoton bidiyo akan wakar da yake yi, yace rashin samun kyaun daukar hoto na bidiyo ya sanya shi koyan yadda ake dauka hoto game da yadda ake editin wakoki da fina-finai.
Ya ce da farko dai kasancewar daukar bidiyon wakokinsa dama nawasu abokan harka na da rauni ya tilasta shi fara daukar hoto, inda a yanzu yake hada waka da daukar hoto, domin kyautata sana’ar sa.
Ya kara da cewa baya ga daukar hoto yanzu babban burinsa bai wuce a gabar da suke ba da yunkurin fito da wani fim da zai nuna rayuwa mawaka ‘yan hip-hop domin al’umma su san cewa suba bata gari bane, kamar kowa suna kokarin nuna al’adar Malam Bahaushe ne.
Tare da kawar da wannan tunanin na suna nuna dabi’un nasara da kuma masu gurbata al’umma, baya ga fadakarwa da kuma nishadantar da mutane, duk kuwa da cewar bincike ya nunan cewar Afrika ma na da ta, ta al’adar, kuma suma suna hip-hop.
Facebook Forum