Ministan bada horo da koyar da ayyukan hannu na jamhuriyar Nijer, ya jagoranci bukin tallafawa matasa maza da mata da yawansu zai kai Miliyan daya da dubu dari biyar da suka fito daga jihahin Agadaze dake arewacin jamhuriyar Nijer. Da kuma Zander dake gabashin kasar.
Shekarun matasan da za su ci moriyar wannan horaswa sun kama daga shekaru goma sha hudu zuwa talatin da shidda, kuma za’a koya masu ayyukanne ta yadda gwamnati zata iya daukar su aiki da kuma yadda zasu iya kasancewa masu dogaro da kai.
Ministan koya ayyukan hannu na jam’uriyar Nijer ya bayyana cewa shirin na daya daga cikin alkawurran da gwamnatin kasar ta dauka na tallafawa matasan Nijer, shi yasa kasar ta nemi tallafi daga kasashe masu hannu da shuni, da kuma kungiyoyi domin tabbatar da aiwatar da wannan yunkuri.
Wannan aiki dai zai lakume kudi kwatankwacin biliyan hudu da rabi na CFA, da tarayyar turai ta soma ba kasar ta Nijer, kuma wannan yunkuri zai taimaka wajan rage yawan kwararar matasa zuwa nahiyar turai da kuma yadda rayuwarsu ke shiga hatsari a hanyar ketarawa kasashen waje.
Ga cikakken ragoton Haruna Mamane Bako daga janhuriyar Nijer.
Facebook Forum