Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanayin Maganar Mutun Na Nuna Alamun Tabuwar Hankali A Tare Da Shi


A wani bincike da masana suka gabatar, wanda yake bayyanar da wasu kadan daga cikin alamun tabuwar hankali. Sun bayyanar da cewar, yadda mutun ke magana na daya daga cikin hanyoyin da za’a iya gane tabuwar hankali a tare da mutun.

A duk lokacin da mutun yake magana, yana tsaye-tsaye don tuna abun da yake son fada, ko kuma mutun na samun matsalar iya tuna wasu abubuwa da suka faru a baya, hakan na iya haifar da wata cuta mai suna ‘Alzheimer’ a turance.

Masanan sunyi gwaji akan wasu mutane, wanda aka kunna musu wani labarin talabijin na wasu abubuwa da suka faru a shekaru biyu da suka gabata, inda aka kasa mutanen gida biyu.

Kashin farko da suke da matsalar tunani, an tambaye su abubuwan da suka faru a fin din a shekaru biyu da suka gabata. Sun dauki lokaci mai tsawo wajen kokarin tuna abun da ya faru.

Su kuwa kashi na biyu, da basu dauke da wata matsala, koda aka tambaye su, sun bayyanar da abun da ya faruk cikin gaggawa. A cewar shugaban binciken Mr. Sterling Johnson na jami’ar Wisconsin Madison, yace a duk lokacin da mutun yake fama da matsala da ta shafi mantuwa, hakan na iya shiga cikin jinsin tabuwar kwakwalwa.

Wannan shine bincike mafi girma da ya jibanci kwakwalwa, wanda aka dauki lokaci mai tsawo ana gudanar da shi. Idan kuma aka kara samun tabbacin cewar hakan yake, to ana iya cewa nesa tazo kusa, wajen magance cutar tabuwar hankali ga milliyoyin al’ummah a fadin duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG