WASHINGTON D.C —
A bangaren hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya kuma, kungiyar kwanlon kafa ta Liverpool, ta shaida wa kungiyar Barcelona, cewar dan wasanta Philippe Coutinho, ba na sayarwa bane, Barcelona ta saka fam miliyan £72 don ganin ta dauke dan wasan
Alvaro Morata na shirin zuwa kungiyar Chelsea, domin duba lafiyarsa kafin ya fara taka leda a kungiyar ta Chelsea. Chelsea da Real Madrid sun cimma yarjejeniya akan sayen dan wasan bisa kudi fam miliyan £70
Facebook Forum