Rundunar ‘yan Sandan birnin tarayyar Najeriya, Abuja, na gudumar Kubwa ta cafke wasu matasa da suka kware wajan sata da barnatar da kayayyaki hukumar jiragen kasa ta Najeriya.
A cewar kakaki rundunar ‘yan Sandan Anjugiri Manzah, matasan da suka shiga hanu sun hada da Uchechi Onyemaizu, mai shekaru 35, Daniel Ugboloke, shekaru 31, da Abdullahi Usman.
Ya kara da cewa jami’an rundunar sun cafke wadannan matasan ne bayan da aka tsegunta masu daidai lokacin da suke tafka ta’asar a tashar jirgin kasa dake Kubwa.
Ya ce za a kara kaimi wajan ganin cewa ana gano sauran kayan karafan da suka sace ya kuma jaddada kudirin rundunar babban birnin tarayyar na tabbatar da tsaro akan duk wasu mahimman kayayyakin gwamnati a birnin da kewaye.
Facebook Forum