Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Aikin Yi, Rashawa, Cin Hanci ke Tura Matasa Ta'addanci


Wasu matasa 'yan Boko Haram da aka kama da aikata ta'addanci a wani lokaci can a baya.
Wasu matasa 'yan Boko Haram da aka kama da aikata ta'addanci a wani lokaci can a baya.

A wani taron karawa juna sani na musamman da aka yi a Lagos aka kara jaddada cewa rashin aikin yi, rashawa, cin hanci ne ke haifar da ta'addanci

A kokarin da ake ci gaba da yi da nufin lalubo hanyoyin samar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro a yankunan arewacin Najeriya masu fama da rigingimu, an yi wani taron karawa juna sani na musamman a birnin Lagos wanda ya samu halartar shugabannin jahohin na arewa masu fama da 'yan ta'adda.

A wajen taron na Lagos an tattauna batutuwa da yawa wadanda suka bayar da damar gano cewa cin hanci da rashawa ne ke hana samar da ayyukan yi ga matasa, wanda hakan kuma shi ne babban abun da ke tura matasan su na shiga ta'addanci kawai domin su samu kudaden kashewa .

Wakilin Sashen Hausa a birnin Ikko, Ladan Ibrahim Ayawa ya halarci taron kuma ga rahoton da ya aiko:

Taron samar da hanyoyin magance ta'addanci a Najeriya - 3'01"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

Jami'ar Colorado ta kasar Amurka da Mujallar Lead ta Najeriya, su ne suka hada guiwa suka shirya taron a birnin Ikko, wanda ya bayar da damar yin musanyar ra'ayi da wasu shugabannin jahohin Arewacin Najeriya dake fama da fitinar ta'addanci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG