Kakakin fadar Kremlin Dimitry Peskov ya shaidawa manema labarai cewar, “mu a matsayinmu na Rasha muna allawadai da wannan mataki, kuma muna da yakinin cewar hakan zai sake ta’azzara al’amura a yankin.”
Ya kara da bayyana damuwar mahukuntan birnin Moscow inda yace, “babban al’amarin shine kai hare-haren bam a kan unguwannin zaman jama’a zai haifar da mummunar asarar rayuka, wacce za ta janyo bala’in neman agaji kamar wanda muke gani a zirrin Gaza.”
Zafafa kai hare-haren da Isra’ila ke yi a kan Hezbollah ya kara damuwar da al’ummar duniya ke da ita game da hatsarin fadadar yakin a yankin Gabas ta Tsakiya wanda ka iya janyo kasar Iran, dake marawa kungiyoyin Hezbollah da Hamas baya.
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana kisan Nasrallah da aka yi a karshen mako a matsayin wanda ke da alaka da siyasa, sannan sanarwar da ma’aikatar wajen Rashan ta fitar ta bukaci Isra’ila da ta gaggauta dakatar da hare-haren da take kaiwa a Lebanon.
-AP/Reuters
Dandalin Mu Tattauna