Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Toshe Hanyoyin Shiga Shafukan Yanar Gizon Muryar Amurka Da Na BBC


Gidan Sadarwar Rasha
Gidan Sadarwar Rasha

Hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta Rasha ta hana shiga gidajen yanar gizo na kafofin labaran kasashen waje da dama da suka hada da BBC da Deutsche Welle saboda yada abin da ta ayyana a matsayin labaran karya, a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan rahotanni kan Ukraine.

Rasha ta sha yin korafin cewa kungiyoyin yada labaran yammacin duniya suna ba da ra'ayi na bangaranci - kuma galibi masu adawa da Rasha - game da duniya yayin da suka kasa rike shugabanninsu da alhakin munanan yake-yaken kasashen waje kamar Iraki da cin hanci da rashawa.

Hukumar ta ce a ranar Juma’a ta toshe gidajen rediyon Muryar Amurka, BBC, Rediyo Free Europe/Radio Liberty, Deutsche Welle da sauran kafafen yada labarai, a cewar kamfanin dillancin labaran Interfax.

BBC ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba.

Wasu mazaunan Rasha ba su iya shiga gidan yanar gizon BBC a ranar Juma'a.

Kamfanin dillancin labaran RIA na kasar Rasha ya ce an takaita amfani da shafukan intanet na sashen Rashanci na BBC da na Rediyo Liberty da kuma kafar yada labarai ta Meduza, inda ta ambaci rajistar hukumar da ke sa ido kan kafafen yada labarai.

A cewar sanarwar da aka samu a hukumance a ranar 3 ga Maris, hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta kasar Rasha ta ce, sashen Rashanci na Rediyon Liberty "babu shakka ya yada labaran bogi game da harin da Rasha ta kai kan yankin Ukraine".

"Irin wadannan bayanan ba daidai ba ne," in ji gidan rediyon Liberty.

Labaran halin da ake ciki a Ukraine ya zama batu mai mahimmanci a Moscow.

Putin ya ce "aikin musamman na soji" na da matukar muhimmanci domin tabbatar da tsaron kasar Rasha bayan da Amurka ta fadada kawancen sojojin NATO a kan iyakokin kasar Rasha tare da goyon bayan shugabannin kasashen yammacin duniya a Kyiv.

Jami'an Rasha ba sa amfani da kalamar "mamaye" kuma sun ce kafofin yada labaran yammacin Turai suna amfani da kalmar "kisan kare dangi" a matsayin harin da Rasha a ke yi a Ukraine.

~ REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG