Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Damu Kan Yadda Ake Nunawa ‘Yan Afirka Wariya Wajen Kwashe Mutane A Ukraine


Wasu daliban Najeriya suna jira a kwashe su a tashar jirgin Lviv da ke Ukraine a ranar Lahadi, 27 Fabrairu, 2022, yayin da dusar kankara ke zuba. (AP Photo/Bernat Armangue)
Wasu daliban Najeriya suna jira a kwashe su a tashar jirgin Lviv da ke Ukraine a ranar Lahadi, 27 Fabrairu, 2022, yayin da dusar kankara ke zuba. (AP Photo/Bernat Armangue)

“Yana da muhimmanci a rika tafiyar da kowa da kowa a matsayin daya, ta hanyar mutuntawa da girmamawa.” In ji Garba Shehu.

Hukumomin Najeriya sun nuna damuwa kan rahotanni da ke nuna cewa ana nunawa ‘yan kasarsu da sauran ‘yan kasashen Afirka wariya yayin da ake kokarin kwashe mutane a Ukraine.

Dubban jama’a a kasar ta Ukraine da ke yankin nahiyar turai na ta ficewa, biyo bayan hare-hare da dakarun Rasha ke kai wa kan biranen kasar yayin da ta takaddama tsakanin kasashen biyu take kara kazancewa.

Gwamnatin Najeriya ta ce akwai ‘yan kasarta kusan dubu hudu a kasra ta Ukraine, galibinsu dalibai da ke zuwa karatu don koyon aikin likitanci.

“Abin da ya kama daga hotunan bidiyo da sahihan rahotanni, zuwa wadanda suke tuntubar ‘yan uwansu da ofishin jakadancin Najeriya, bayanai na nuni da cewa ‘yan sandan Ukraine da jami’an tsaro na hana ‘yan Najeriya hawa motocin bas-bas da jiragen kasa zuwa kan iyakar kasar ta Ukraine da Poland.” Kakakin Shugaba Buhari Malam Garba Shehu ya fada cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Wasu 'yan kasashen Afirka suna jira a kwashe su a filin jirgin kasa na Lviv yayin da rikicin Ukraine ya kazanta. (AP Photo/Bernat Armangue)n
Wasu 'yan kasashen Afirka suna jira a kwashe su a filin jirgin kasa na Lviv yayin da rikicin Ukraine ya kazanta. (AP Photo/Bernat Armangue)n

“A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga yadda aka tilastawa wata uwa ‘yar Najeriya da jaririnta tashi daga wajen zamanta don wani ya zauna.” Sanarwar Garbe Shehu ta kara da cewa.

A cewar kakakin na Buhari, akwai wasu rahotanni da ke nuna cewa ‘yan sandan Poland na hana ‘yan Najeriyar shiga Poland daga Ukraine.”

Gwamnatin Najeriya, Shehu ya ce, ta fahimci irin wahala da fargaba da ke fuskantar mutanen da suka tsinci kansu cikin wannan yanayi mai ban tsoro, ta kuma jinjinawa wadannan jami’an tsaro da na kan iyaka.

“Amma, yana da muhimmanci a rika tafiyar da kowa da kowa a matsayin daya ta hanyar mutuntawa da girmamawa.” In ji Shehu.

Wasu daliban Najeriya suna jiran sakamakon gwajin cutar COVID-19 yayin da suka tsallaka zuwa Hungary daga Ukraine. (AP Photo/Anna Szilagyi)
Wasu daliban Najeriya suna jiran sakamakon gwajin cutar COVID-19 yayin da suka tsallaka zuwa Hungary daga Ukraine. (AP Photo/Anna Szilagyi)

Kokarin neman martanin hukumomin Ukraine kan wannan lamari ya ci tura, sai dai wata sanarwa da ma’aikatar harkokin Najeriya ta fitar a ranar Lahadi, ta nuna cewa ana samun kyautatuwar al’amura.

“Ministan harkokin waje (na Najeriya) ya tattauna da takwaransa na Ukraine kan wannan lamari, kuma dukkansu sun dukufa wajen neman yadda za a saukakawa ‘yan Najeriya da sauran ‘yan wasu kasashen wajen samun hanyar ficewa.” Sanarwar mai dauke da sa hannun Ambasada Gabriel Aduda ta ce.

A halin da ake ciki, ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta ce, kasashen Romania da Hungary sun amince su ba ‘yan Najeriya da suka fito daga Ukraine, damar shiga kasar ba tare da tarkdun visa ba.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Lahadi ta ce mutum dubu 200 ne suka fice daga Ukraine inda rabin wannan adadi ya tsallaka zuwa kasar Poland da ke makwabtaka.

Ana kuma fargabar adadin zai kai miliyan hudu idan lamarin ya ci gaba da kazancewa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG