Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Limaman Coci Shida A Jihar Anambra


Nigeria Boko Haram Corruption
Nigeria Boko Haram Corruption

Al’amarin ya faru ne a ranar 1 ga watan nan na Mayu kamar yadda rahotanni suka nuna amma har ya zuwa ranar Lahadi ba a ji duriyarsu ba.

Rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu limaman Coci shida yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Awka na jihar Anambra a kudu maso gabashin Najeriya.

Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan bindigar sun sace Archbishop Uka Uka na Mujami’ar Brotherhood of the Cross and Star, (BCS) da matarsa Anne Osim da dansu Ronald Uka Osim.

Sauran limaman Cocin sun hada da Azuka Ochu, Moses Okafor da Anderson Akwazie a cewar jaridar Daily Trust.

Jaridar Daily Post ta yanar gizo ta ruwaito cewa mutanen na hanyarsu ta zuwa Awka ne daga jihar Abia don gudanar da ayyukan wa’azi a lokacin da lamarin ya faru.

Al’amarin ya faru ne a ranar 1 ga watan nan na Mayu kamar yadda rahotanni suka nuna.

“Mun damu matuka, amma muna da tabbacin cewa Ubangijin da suke bautawa zai taimaka musu.” Jaridar ta Daily Post ta ruwaito wani Limami a Cocin ta BCS, Bishop Denis Onuoha yana cewa.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, ta ce ba ta da masaniyar aukuwar wannan al’amari.

“Ba mu da wasu bayanai da suka nuna aukuwar wannan al’amari a jihar Anambra.” Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce a ranar Asabar dauke da sa hannun Kakakinta SP Tochukwu Ikenga.

Sanarwar ta kara da cewa, “muna kira ga jama’a da su taimaka mana da bayanai kan wannan al’amari idan har ya faru, hakan zai ba mu dama mu kaddamar da bincike.”

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG