A wani jawabin telbijin da Putin yayi a wani taron manema labarai a jiya Lahadi a India, yace zancen tuhumar kutsen sakonnin email, wani kokari ne da hukumomin na Amurka ke yi don janye hankalin Amurkawa daga abinda ya kira “tarin matsalolin” da Amurka ke fama dasu.
Kalaman na Putin sun zo ne kasa da kwanaki biyu da mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya aike da sakon kashedi ga Shugaba Putin.
Mr. Biden ya shaidawa tashar telebijin ta NBC a ranar Juma’a cewa, ramuwar gayya da Amurka zata yi a kan harin yanar gizo da da Rasha ke yiwa Amurka, zai zo a lokaci na zabin ransu kuma daidan lokaci da zai yi babban tasiri.