Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Netherlands Geert Wilders Zai Gurfana Gaban Kotu Bisa Kalamun Kiyayya Ga Musulmi


Wasu Musulmai da suka shiga zanga zangar kin amincewa da sanya hijabi
Wasu Musulmai da suka shiga zanga zangar kin amincewa da sanya hijabi

A yau Juma’a, wata kotu a kasar Netherland ta ce masu shigar da kara a kasar, za su iya gabatar da kokensu akan wani dan siyasar kasar Geert Wilders, wanda ake zargin da furta kalaman nuna kiyayya ga Musulmi.

A wani zaman farko da aka yi a watan da ya gabata, Wilders da lauyoyinsa suka nemi alkalai su yi watsi da korafe-korafen da aka gabatar a gabansu, inda suka ce karar bita-da-kullin siyasa ce, wacce aka shirya domin a kassara takararsa a zaben da za a yi a watan Maris mai zuwa.

Sai dai a hukuncin farko da ya yanke, alkalin kotu a gundumar Hague, ya yi watsi da hujjar Wilders, inda ya ce shari’ar ba za ta shafi walwalar siyasarsa ba, ko kuma jam’iyyarsa ta Freedom Party.

Wannan kara da aka shigar akan Wilders ta samo asali ne daga wasu kamalamai da ya furta a shekarar 2014 a lokacin yakin neman zabe a Hague, inda ya tambayi magoya bayansa ko suna so baki ‘yan kasar Morocco da yawa su shiga kasar ko kuma akasin hakan?

Nan take dai magoya bayansa suka ce kadan su ke bukata, shi kuma Wilders ya ce, za a shirya yadda za a aiwatar da hakan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG