Yanzu an sa ido a gani ko idan Trump ya sha kaye a hannun yar takarar Democrat Hillary Clinton a zaben na ranar takwas ga watan Nuwamba, ko zai amince da shan kayen ne ko kuma dai zai ci gaba da korafin an masa magudi ne.
Idan kuwa Trump yaki yin jawabin bayyana amincewarsa ga rashin nasara, zai gurgunta tsohuwar akidar siyasar Amurka ta shekara da shekaru da aka saba da ita.
Ko a shekarar 2000, lokacin da aka yi zaben da ba a taba samun mai tarin rigingimmu kamar shi ba, dan takarar jami’iyar Democrat Al Gore ya amince da nasarar dan takarar jam’iyyar Republican George W. Bush, bayan da kotun koli ta dakatar da kirga kuri’u a jihar Florida, ta kuma tabattar da nasarar Mr. Bush.