Kungiyar Syrian Observatory for Human rights ta ruwaito a yau juma’a cewa an kaddamar da hare-haren sama da dama a gabashin Aleppo, kuma bayan an kammala kai hare-haren zuwa tsakiyar safiya, an ci gaba da wasu daidaikun hare-hare a arewaci da kudancin birnin na Aleppo.
Wasu majiyoyi na ‘yan fafatuka, sun ce hare-haren sun kashe ko kuma sun raunata mutane da dama, koda ya ke babu takamaiman adadin mutanen da suka jikkata, domin har yanzu akwai wadanda su ke karkashin baragizan gine-gine.
Wadannan sabbin hare-hare, na zuwa ne kwana guda bayan da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ke shirin ganawa da takwaran aikinsa na Rasha Sergie Lavrov.
Kuma wannan ganawa ita za ta kasance ta farko, tun bayan da Hukumomin Washington da Moscow su ka yanke tattaunawar diplomasiyya a farkon watan nan.