Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha: Shugaban ‘Yan Adawa Alexei Navalny Ya Mutu A Gidan Yari


Alexei Navalny
Alexei Navalny

Hukumar kula da gidajen yari  a Rasha ta fada a wata sanarwa cewa Navalny ya kamu da rashin lafiya bayan da ya dawo daga wani dan tattaki da ya yi don mike kafa, inda daga baya ya yanke jiki ya fadi.

Madugun ‘yan adawa a Rasha, Alexei Navalny ya mutu a cewar hukumar da ke kula da gijane yari a kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa Navalny ya rasu ne a ranar Juma’a yayin da yake tsare a gidan yari.

Ya mutu yana da shekaru 47.

Navalny wanda ya kasance babban dan adawar Shugaba Vladimir Putin ya sha shirya manyan-manyan zanga-zangar adawa da fadar gwamnatin Kremlin.

Ya kuma sha shirya gangamin yaki da batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa da abin da ya kan kira mulkin kama karya.

Hukumar kula da gidajen yari a Rasha ta fada a wata sanarwa cewa Navalny ya kamu da rashin lafiya ne bayan da ya dawo daga wani dan tattaki da ya yi don mike kafa, inda daga baya ya yanke jiki ya fadi.

Nan take aka kira motar daukan marasa lafiya don a duba shi, amma sai rai ya yi halinsa, ta kara da cewa.

Mai magana da yawun Navalny, Kira Yarmysh, ta fada shafin X cewa tawagar mukarrabansa ba su samu cikakken bayani kan mutuwarsa ba amma lauyansa ya kama hanyar zuwa garin da ake tsare da shi.

Navalny na tsare ne a gidan yari bayan da aka yanke masa hukuncin shekaru 19 saboda tuhuma da aka masa kan nuna tsattsauran ra’ayi.

A watan Disamba aka mayar da shi wani gidan yari na musamman mai tsauraran matakan tsaro daga wani gidan gyara hali da ke yankin tsakiyar Rasha.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG