Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Gana Da Vladimir Putin


A karon farko tun bayan da aka rantsar da shi, shugaban Amurka Joe Biden ya yi magana da shugaban Rasha Vladimir Putin, inda ya bayyana damuwar Amurka kan wasu batutuwa.

Daga cikinsu akwai batun kama madugun ‘yan adawar Rasha, Alexei Navalny, da leken asirin da Moscow ke yi ta yanar gizo, da kuma biyan kudi masu tsoka don kashe sojojin Amurka a Afghanistan, a cewar wasu manyan jami’an gwamnatin Biden biyu.

Matsayar Biden na nuna wata alamar canji na nan take akan yadda tsohon shugaba Donald Trump ya yi harkokinsu da Rasha, wanda yawancin lokuta ya ke bayyana jin dadinsa akan kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsa da shugaban Rasha.

A gefe guda, a cewar bayanan hirar wayar daga bangaren Amurka, Biden ya fadawa Putin cewa ya kamata Rasha da Amurka su kammala tsawaita yarjejeniyar makaman nukiliya ta shekara 5 kafin karewar wa’adinta a farkon watan Fabrairu.

Nan take dai ba a samu bayanan tattaunar wayar daga Moscow ba, amma Rasha ce ta fara tuntubar Biden a farkon kwanakin wa’adinsa na shekaru hudu a Fadar White House.

XS
SM
MD
LG