Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Mayar Da Navalny Birnin Berlin a Jamus


Wata motar daukan marasa lafiya da ake ganin ita ta dauki Navalny yayin da aka isa da shi birnin Berlin na Jamus. Aug.22, 2020.
Wata motar daukan marasa lafiya da ake ganin ita ta dauki Navalny yayin da aka isa da shi birnin Berlin na Jamus. Aug.22, 2020.

Wani jirgin sama dauke shugaban ‘yan adawar kasar Rasha Alexie Navalny wanda ba ya cikin hayyacinsa, bayan da aka yi zargin saka masa guba, ya sauka a Berlin a yau Asabar.

Navalny zai samu kulawa ne a asibiti mafi girma a birnin na Berlin.

Gabanin hakan, likitocin Rasha sun amince da bukatar da aka gabatar musu ne ta a je a nema masa magani a Jamus – abin da ya kawo karshen takaddamar da ake ta yi ta wanda ya kamata ya ba shi kulawa – bayan da iyalansa suka yi zargin cewa da gangan aka yi yunkurin saka masa guba a Siberia a farkon makon nan.

A ranar Juma’a wani likita a asibitin birnin Omsk da aka fara kwantar da Navalny, ya ce, “jikinsa da sauki,” bayan da aka yi masa allurar da ta fitar da shi daga cikin hayyacinsa, aka kuma saka masa na’urar taimakawa numfashi.

Matakin amincewa a kai shi wani asibiti a kasashen ketare ya biyo bayan bukatar da mai dakinsa Yulia Navalnaya ta mika ga shugaba Vladimir Putin ta kafar yanar gizo, wacce ta nemi a samar da shirin fita da shi domin neman magani.

Hukumomin Rasha sun ce za su kaddamar da bincike don gano ko da gaske ne guba aka sakawa Navalny, wanda ya kasnace mai yawan sukar lamirin hukumomin Rasha.

Navalny ya sha jagorantar zanga zangar adawa da gwamnati, lamarin da ya sa aka sha kulle shi a gidan kurkuku.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG