Navalny mai shekaru 44 da haihuwa, ya so ya yi fatan rage karfin jam’iyyar ta United Russia a madafun iko, ya kuma yi kira ga magoya bayan sa da su yi zaben kawar da haka a kaikaice, kafin ya kwanta rashin lafiya mai tsanani, akan abin da Jamus da sauran kawayensa suka ce yunkuri ne na kashe shi a watan da ya gabata.
Jam’iyyar ta United Russia da ke goyon bayan shugaba Vladimir Putin, ta mamaye siyasar yankin, to amma zaben na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a suka fusata akan tsawon shekaru na tabarbarewar tattalin arziki, da kuma yadda gwamnati ta tunkari annobar coronavirus.
Za’a zabi gwamnoni 18 da kuma ‘yan majalisar yankuna da na birane, a zaben wanda ake kallo a matsayin zakaran gwajin dafi na zaben majalisar dokoki da za’a gudanar a watan Satumba.
An soma zaben ne tun a ranar Juma’a bayan da hukumomi suka fadada zabe cikin kwananki uku, wani yunkuri da kungiyar Golos mai sa ido akan zabe ta yi suka akan sa, tare da yin gargadin cewa tsawon lokacin da za’a dauka na gudanar da zaben, kan iya haifarda wahalar gaske ga masu sa ido su gano magudi a rumfunan zabe.
Facebook Forum