‘Yan sandan kasar Rasha sun kulle masu zanga-zanga sama da 3,000 a ranar Lahadi, yayin da masu goyon bayan Alexei Navalny mai caccakar gwamnatin Rasha da aka kulle suka tattaru kan titina a karshen mako na biyu suna neman a sako shi a cewar OVD-Info, wata kungiyar sa ido.
Abokan huldar Navalny sun sake yin kira da a yi gangami a fadin kasar gabanin shari’arsa da za a fara ranar Talata 2 ga watan Fabarairu.
Zanga-zanga ta farko an yi ta ne a Siberia da yankin Far East na Rasha, ciki har da birnin Vladivostok, inda masu zanga zangar suka yi watsi da yiwuwar kamen ‘yan sanda da kuma tuhumarsu da aikata babban laifi.
A yankin Novosibirsk da ke Siberia, dubban masu zanga-zanga sun dunguma kan titina suna fadin "Putin, barawo!" ga dukkan alamu suna nufin batun fadar yankin tekun Bahar Asuwad da aka yi zargin shugaban Rasha Vladimir Putin aka ginawa da kudin gwamnati.