Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan adawa sun ce an hallaka mutane da dama a kasar Sham


Gawarwakin wasu mutane a birnin Alepo
Gawarwakin wasu mutane a birnin Alepo

Gidan talabijin din Syria ko Sham y ace an hallaka akallan mutane 25

Gidan talabijin din Syria ko Sham y ace an hallaka akallan mutane 25 aka kuma raunata wasu 175 a wasu fashe-fashe biyu a birnin Aleppo da ke arewacin kasar a yau dinnan Jumma’a.

An auna bama-baman ne kan wani ginin hukumar sojoji masu binciken sirri da kuma wani sansanin jami’an tsaro da ke babban birnin na hada-hadar kasuwancin Sham, wanda kafin nan ya kasance kusan cikin kwanciyar hankali tun bayan soma boren kyamar manufofin gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad da ya barke a cikin watan Maris.

Gidan talabijin mallakin gwamnatin Sham na zargin ‘yan ta’adda masu dauke da makami da kai harin, inda ya nuna hotunan biyon gawarwaki jina-jina a daddatse a wajen gine-ginen da aka masu kaca-kaca.

A birnin Homs na yankin tsakiyar kasar, ‘yan rajin kare hakkin dan adam na Sham sun ce yau kwana bakwai kenan aka yi ana ta girke tankokin gwamnati daura da unguwar ‘yan adawa a cigaba da amfani da karfin da gwamnati ke yi wajen murkushe boren a fadin kasar.

‘Yan fafatika sun ce an hallaka daruruwan mutane tun bayan da aka fara kai hari kan Homs da safiyar ranar Asabar.

XS
SM
MD
LG