Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Jakadancin Amurka Ya Yaye Wasu Matasan YALI Bayan Samun Horo Ta Yanar Gizo


YALI
YALI

Ofishin jakadancin Amurka a jamhuriyar Nijer ya yaye wasu matasa kimanin 45 wadanda suka kammala daukan horon watanni 3 a kan dubarun kafa masana'antu da shugabancin harakokin jama'a kamar yadda aka saba a karkashin shirin tsohon shugaban Amurka Barack Obama.

Gomman matasan da suka fito daga sassan Nijer ne suka samu wannan horo a karkashin shirin YALI na shugaba B. Obama wanda aka gudanar a tsawon makwanni inda kwararu daga jami’o'in Amurka suka bada darusan da suka shafi sha’anin kafa masana’antu da hikiomin tafiyar da su da kuma yadda ake shugabancin harakokin jama’a.

Moussa Chehou na daga cikin wadanda suka samu takardar shaidar lakantar wannan fanni a yayin wani kwarkwaryan bukin da aka shirya a cibiyar raya al’adun Amurka.

Sabanin yadda ake tattara matasa kasar Amurka ko birnin Dakar na Senegal domin samun irin wannan horo a bana abubuwa sun gudana ne ta yanar gizo sanadiyar anobar COVID-19, kuma a cewar magatardar kungiyar matasan YALI Marichatou Samira Amadou an samu nasarori fiye da yadda ake zato.

Daga lokacin bullo da shirin shugaba Barack Obama a 2010 kawo yau daruruwan matasan Nijer suka ci moriyar wannan tsari mai hangen baiwa matasan Afrika damar bada gudunmuwa a aiyukan ci gaban wannan nahiya ta yadda zasu ba da misalai ga kannunsu kwatankwacin bajintar da aka gani a wajen wasu daga cikin shugabanin da suka gabata wadanda komai nasu ya ta'allaka a kan maganar fitar wannan nahiya daga ramin da tsinci kanta ciki.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG