Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Jakadancin Amurka Ya Yaba Da Zaben Nijar


Ofishin jakadancin Amurka da ke Yamai, babban birnin Nijar, ya yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki cikin lumana.

A ranar 27 ga watan nan na Disamba ne al’umar kasar ta dunguma zuwa rumfunan zabe don kada kuri’a a zabukan biyu.

“Muna taya al’umar Nijar da suka samu damar aiwatar da ‘yancinsu na dimokradiyya wajen zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki murna,” a cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizon ofishin jakadancin na Amurka a ranar Litinin.

Masu Aikin Sa Ido a Zaben Nijar Daga Kasashen Afirka.
Masu Aikin Sa Ido a Zaben Nijar Daga Kasashen Afirka.

Sanarwar ta kara da cewa masu sa ido kan zabe da ofishin jakadancin ya tura, sun ce an yi zaben cikin lumana da kuma tsari.

“Mun kuma lura da cewa an samu ci gaba wajen bude rumfunan zabe akan kari da kuma wadatar kayan aiki, an kuma samu karin mutane da suka saka takunkumi. Muna kira ga ‘yan Nijar, da su ci gaba da daukar matakan dakile yaduwar cutar COVID-19 da muhimmanci,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyu da su yi amfani da matakan da shari’a ta samar wajen yin sulhu kan rikicin zabe, su kuma yi kira ga magoya bayansu da su zama masu hakuri iya tsawon lokacin da za a tantance sahihancin zaben, su kuma bi kadinsu cikin lumana kuma ta hanyar da shari’a ta tanada.”

“Amurka za ta ci gaba da dukufa wajen karfafa mulkin dimokradiyya da kungiyoyin fararen hula. Muna kira ga al’umar Nijar da ta ci gaba da nuna goyon baya ga tsarin dimokradiyya da ‘yancin fadin albarkacin baki, yin cudanya, da kuma yin taruka," a cewar sanarwar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG