Bikin sallah a arewacin Najeriya wani dama ne da shugabanni kan yi anfani da shi domin duba yanayin da kasa da kuma 'yan kasa ke ciki tare da yin tanbihi da kuma janyo hankalin dubun dubatan jama'a dake tattaruwa wajen bikin dangane da samar da hanyoyin ci gaba.
A wannan karon kalamun nuna kiyayya tsakanin 'yan arewa da 'yan kabilar Igbo dake hankoron kafa kasar Biafra su ne suka fi jan hankalin gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari.
A sakonsa na sallah ya waiwayi baya dangane da hadewar kudanci da arewacin Najeriya zama kasa daya da kuma barazanar darewa da kasar take fuskant yanzu haka.
Ya na mai cewa hade arewa da kudu yau shekara 100 kenan ya na mai jaddada cewa "ko aure aka yi ya kai har shekara 20 ko 30 kana a ce zai rabu, yin hakan na da wuya balantana a ce auren da ya fi shekaru 100 ana yi."
Masari ya ce wadanda suke da ruwa da tsaki a kasar sun amince cewa basu yadda ma wani ya kawo maganar raba gari ba.
Shi ko kuwa girma sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman sakonsa na sallah tamkar wa'azi ne.
Ya ce halayyar 'yan Najeriya ita ce musabbabin duk matsalolin da suke fuskanta.
Ya ce Allah ba zai kawo sassauci ba sai 'yan Najeriya sun sake halinsu saboda yanzu babu abun da suka sa gaba illa samun duniya da cutar juna da yin karya da kashe-kashe.
Sarkin ya nuna takaicinsa da yadda 'yan arewa suka yi watsi da ayyukan noma suka koma ga harkokin man fetur domin samun kudin sauki.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.
Facebook Forum