Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Matasan Arewa Su Kasance Masu Sauraren Manya


Aiwatar da aiyuka bisa tsoron Allah da cigaba da kasancewa ana yin adalci ga juna zai tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'umomi.

A cikin hudubarsa na sallar Eid Fitr, wanda aka gudanar a Masallaci idi na unguwar Ojo, a birnin Ibadan Sheikh Ibrahim Suleman, ya tunadar da jama’a musulmi tsoron Allah ta yadda za a gujewa zalunci da tauye hakkin ja,ma’a.

Ya kuma umarci jama’a da su cigaba da kyawawan dabi’o da suka gudabar a cikin wata Azumin da ya gabata domin kasancewa ana kusantar Allah a kowane lokaci.

A nasa jawabin Sarkin Hausawan Ojo Ibadan, Alhaji Ali Yaro, ya yi kira ga matasan arewacin Najeriya, da su kasance masu jin shawaran Sarakuna da mayan dattawa da fatan Allah yasa Najeriya ta zauna lafiya.

Ya kuma kara da kira ga sarakunan hausawa mazauna yammacin Najeriya, sun tabbatar da cewa sun nemi hadin kan ga al’umarsu na zaman lafiya domin hana afkuwar irin abinda ya faru a garin Ile Ife.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG